1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila da Falasɗinu sun hau teburin sulhu

March 18, 2012

Hukumomin Falasɗinu dana Isra'ila suna tattauna batutuwan da suka shafi haraji a tsakanin su.

https://p.dw.com/p/14MXs
Israeli Prime Minister Benjamin Netanyahu shakes hands with Palestinian president Mahmoud Abbas, at his residence in Jerusalem, Israel Wednesday, Sept. 15, 2010. Clinton is in the region for Mideast peace talks. U.S. Secretary of State Hillary Rodham Clinton on Wednesday said Israeli and Palestinian leaders are "getting down to business" on core issues of renewed peace talks, but gave no sign they are any closer to resolving a looming crisis over Israeli West Bank settlements. (AP Photo/Alex Brandon, Pool)
Firaministan Isra'ila Netanjahu da shugaba Abbas na FalasɗinuHoto: AP

Hukumomin Isra'ila dana Falasɗinu suna gudanar da tattaunawar da ta shafi tattalin arziƙi a tsakanin su duk kuwa da jinginar da tattaunawa da ta shafi zaman lafiya, a wani matakin sake warware batun harajin Falasɗinu da Isra'ila ke karɓa a madadin hukumar Falasɗinawa gabannin ta miƙa mata. Jami'an da suka sanar da hakan sun ƙara da cewar matakin zai taimakawa gwamnatin Falasɗinu shawo kan matsalar bashin dake kanta. Tun bayan da Isra'ila ta mamaye gaɓar tekun Jordan a shekara ta 1967 ne sassan biyu suka cimma wata yarjejeniyar wucin gadin da ta tanadi Isra'ila ta karɓi harajin daya shafi harkokin Kwastam a madadin Falasɗinu, wanda kuma ya kai na kuɗi dalar Amirka miliyan 100 a kowane wata akan kayayyakin da aka shigo da su daga yankunan.

Sai dai kuma Isra'ila ta dakatar da miƙawa Falasɗinu harajin nata a lokacin da sassan biyu suka fuskanci taƙaddamar diflomasiyya da kuma na tsaro, abinda kuma ya janyo Allah wadai daga ƙasashen duniya daban daban. A tsokacin daya yi game da taron, ministan kuɗin Isra'ila Yuval Steinitz ya shaidawa maneman labarai cewar, ko da shike lamarin na da matuƙar wahala, amma yana fatan taron zai cimma nasara domin amfanar sassan biyu, wato Isra'la da Falasɗinu.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Zainab Mohammed Abubakar