1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila da kuma Hamas na kan bakarsu

August 10, 2014

Ana kwan- gaba kwan- baya a taron sulhu da ke gudana a Masar tsakanin Isra'ila da kuma Hamas inda bangarorin biyu suke karar tsaye ga shirin tsagaita bude wuta.

https://p.dw.com/p/1Cs24
Hoto: Reuters

Gwamnatin Isra'ila da Kungiyar Hamas na ci gaba da jajircewa a kan matsayinsu a taron da ke gudana a Masar da nufin sulhunta rikicin da sassa biyu ke fama da shi. Wakilan Falesdinu sun yi barazanar fitsewa daga zauren taron a wannan Lahadi idan Isra'ila ba ta aiko da wakilanta ba. Yayin da a nata bangaren Isra'ila ta ce ba za ta shiga a dama da ita ba, matikar Hamas ba ta dakatar da rokokin da take harba mata ba.

Sassan biyu dai sun koma gidan jiya, inda Hamas ta ke harba rokoki zuwa Isra'ila, yayin da dakarun Isra'ila ke kai farmaki a zirin Gaza. Wani Bafalesdine daya ya rasa ransa a safiyar wannan Lahadin, yayin da wasu fararen hula bakwai kuma suka jikata, bayan da sojin Isra'ila suka kai hari.

Kasashen Jamus da Faransa da kuma Birtaniya sun yi kira ga bangarorin biyu da ke gaba da juna a da kai hankali nesa tare da cimma sabuwar yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Fiye da mutane dubu da 900 suka rasa rayukansu a wannan rikicim galibinsu Falesdinawa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita. Suleiman Babayo