1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila: Dakatar da sake fasalin shari'a

March 28, 2023

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya sanar da dakatar da kudurinsa na sake fasalin bangaren shari'ar kasar zuwa wani lokaci domin kaucewar barkewar yakin basasa.

https://p.dw.com/p/4PLMP
Firanministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu
Hoto: Marc Israel Sellem/AFP

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sanar da dakatar da kudurinsa na sake fasalin fanin shari'ar kasar zuwa nan da wani lokaci domin sake tattaunawa kan kudurin da ya haifar da cece-kuce.

Ministan tsaron kasar Itamar Ben-Gvir ya yi maraba da matakin da Netanyahu ya dauka na jinkirta sauyin har zuwa karshen watan Afrilun wannan shekarar.

Ita ma fadar mulkin Amirka ta White House ta nuna gamsuwarta na dakatar da kudurin wanda zai bada damar samun isashen lokacin kara yin bita a kai.

Sanarwar hakan dai na zuwa ne yayin da dubban 'yan Isra'ila ke zanga-zangar nuna adawa da garambawul din da gwamnatin kasar ke shirin yiwa fannin shari'a.