1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tserewar Falasdinawa daga kurkuku

Mahmud Yaya Azare LMJ
September 7, 2021

Bayan da wasu fursinoni Falasdinawa shida suka tsere daga gidan yarin Jalbu na Isra'ila da ke da tsanannain tsaro, jami'an tsaron Isra'ilan na ci gaba da neman Falasdinawan ruwa a jallo.

https://p.dw.com/p/402qu
Gefängnisausbruch in Israel
Jami'an tsaron Isra'ila, na yin nazarin ramin da fursinoni Falasdinawa suka biHoto: Sebastian Scheiner/AP/picture alliance

Wadannan fursinoni Falasdinwa dai, sun yi nasarar tserewa daga gidan yarin na Jalbu a Isra'ila, bayan da suka haka rami a karkashin kasa daga bandaki. Dubban Falalsdinawa a birnin Jenin na yankin Falasdinu na ta shagulgulan murna, kan tserewar 'ya'yansu shida daga gidan yarin na Isra'ila na Jalbu da ke dajin kare-kukanka, wanda Isra'ila ke tsare masu zaman daurin rai-da-rai da take ganin suna da matukar hadari.

Karin Bayani: Damuwa kan rikicin Isra'ila da Falasdinawa

Wani kusa a kungiyar Jihad al-Islami da 'yan kungiyar tasu shida suka tsere daga gidan yarin, ya ce wannan babbar bushara ce ta 'yantuwar Falalsdinu. Ita ma mahaifiyar guda daga cikin wadanda suka tseren, kira take ga sauran fursinonin da subi sawun danta wajen 'yanta kansu. Shugaban gidajen yarin arewacin Isra'ilan da ke tsaye a gaban ramin da fursinonin suka yi wa bugun da ya  ba su damar fita domin tserewa, ya siffanta tserewar da mummunar baraka ga lamarin tsaron gidan yarin. 

Gidan talabijin na Isra'ilan dai, ya nuna hotunan karshe  da kyamarar gidan yarin ta dauka na fursinonin shida suna kai wa suna komawa a cikin gidan yarin, kafin su yi batan dabo. Ana zaton fursinonin Falasdinun sun yi anfani da cokulan cin abincin da ake ba su ne, wajen haka ramin mai tsayin mita 25, kasancewa ba a barin masu ziyarar su shiga da ko da tsinke ne. 'Yar sandar Isra'ilan da ke kan hasumiyar duba farfajiya da wajen gidan yarin dai, ta fadawa masu bincike cewa gyangyadi ya yi ta kwasheta a daren da fursinonin suka tsere. Idan ana iya tunawa dai, a shekarar 1986 ne wasu fursinonin Falasdinawa suka tsere daga gidan yarin Zirin Gaza, lamarin da ya zama masomar tilastawa Isra'ilan ficewa daga Zirin na Gaza.