An kai sabon hari da rokoki a Isra'ila
March 25, 2019Talla
Mazauna yankunan arewacin birnin Tel Aviv sun bayyana yadda karar harbe-harben bindigogi da ababen fashewa suka tashesu daga bacci, amma sojojin Isra'ilal na zargin Falasdinawa da haddasa gobara bayan harba rokoki da suka fashe kan wani gida a garin Mishmerat.
Akwai fargabar Isra'ila za ta maida martani kan sabon harin, inda firaiministan kasar Benjamin Netanyahu da ke ziyara a kasar Amirka ya sanar da shirinsa na katse ziyararsa in ya gama da Shugaba Trump zuwa jimawa don komawa Isra'ila din da nufin tinkarar batun.
Sake barkewar rikici tsakanin Faladsinawa da Isra'ila na jefa faregaba ga makomar zaben Isra'ilan da zai gudana a ranar 9 ga watan gobe, zaben da ake ganin Netanyahu na fuskantar kalubale daga 'yan adawa kan zargin cin hanci.