1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila na fargabar Hamas za ta zamo `yar korar Iran.

February 24, 2006

A halin da ake ciki yanzu, jami'an gwamnatin Isra'ila na bayyana damuwarsu game da yunƙurin da Ƙungiyar Hamas ke yi na samun taimako daga Iran. Tun makon da ya gabata ne dai gwamnatin Firamiya Olmert ta riƙon ƙwarya a Isra'ilan ta ce za ta dakatad da biya wa Hukumar Falasɗinawan duk wasu kuɗaɗen fito da na haraji da take karɓa a madadinta.

https://p.dw.com/p/Bu1S
Shugaban Hamas Khaled Mashaal da shugaba Ahmadinijad na Iran, yayin ziyararsa a birnin Teheran.
Shugaban Hamas Khaled Mashaal da shugaba Ahmadinijad na Iran, yayin ziyararsa a birnin Teheran.Hoto: AP

Mafi yawan Isra’ilawa dai na nuna goyon bayansu ga shawarar da gwamnatin Firamiyan riƙon ƙwarya Olmert ta yanke, wato ta riƙe kuɗaɗen fito da na haraji da ya kamata ta biya wa hukumar Falasdinawa, wanda yawansu ya kai dola miliyan 50 a ko wane wata. Ko Alon Liel, wani ɗan siyasan Isra’ilan mai sassaucin ra’ayi ma, wanda kuma ya taɓa aiki a ma’aikatar harkokin wajen Isra’ilan tamkar babban sakatare a shekara ta 2001, ya nuna goyon bayansa ga matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka. Amma a nasa ganin, ba amincewar Hamas da gwamnatin Isra’ilan ne abin da ya fi damun yan ƙasar bani Yahudun ba. Bisa cewarsa dai:-

„Idan Hamas ta canza manufofinta, har ta iya kafa gwamnati…, ba na batun yin shawarwari da su a nan, ko ma amincewa da Isra’ila…, idan gwamnatin da za ta kafa ta nuna halayyar kirki ta yadda ba za mu yi wata fargaba game da ita ba, idan muka tabbatar cewa, ba ƙungiya ce ta ta’addanci ba, to ina zaton za a dinga tura musu kuɗin, ba ma daga gare mu kawai ba, har ma daga gamayyar ƙasa da ƙasa.“

A shekarar bara dai, Falasɗinawa sun sami taimakon kuɗi na kimanin dola biliyan ɗaya da digo ɗaya daga ƙetare. Rabin wannan adadin ya fito ne daga Ƙungiyar Haɗin Kan Turai, sa’annan kusan rubu’i kuma daga Amirka. Sauran kuma suna zuwa ne daga ƙasar Norway, da bankin duniya da ƙasashen Larabawa. Amma tun da Hamas ta lashe zaben Falasdinawan ne shugaba Bush ya ce ba zai bai wa Hukumarsu tallafin kudin da Amirkan ke bayarwa ba. A nan Turai dai, har ila yau ba tsai da wata shawwara a hukumance ba tukuna. Babban jami’in Ƙungiyar Haɗin Kan Turan, mai kula da batutuwan harkokin waje, Javier Solana, ya tabbatar cewa, ko da Hamas ma ta hau kan mulki, za a ci gaba da bai wa Falasdinawan taimakon agaji.

A nasa ɓangaren, shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas, ya yi garegaɗin cewa, hukumar Falasɗinawan za ta huskanci wani matsi na tattalin arziki, idan gamayyar ƙasa da ƙasa ta dakatad da taimakon da take ba ta. Wani babban jami’in Hukumar mai kula harkokin kuɗi, Maher al-Masri, shi ma ya sake nanata jawabin da Mahmud Abbas ya yi. Ya kuma yi kira ga Isra’ilan da ta bi ƙa’idojin yarjejeniyar nan ta Oslo, ta saki kuɗaɗen Falasɗinawan da ta riƙe. Kamar dai yadda ya bayyanar:-

Ko wane ne ma ke mulki, ai wannan kuɗin dai na Hukumar Falasɗinawa ne. Sabili da haka, kamata ya yi a saki kuɗin. Bai dace ba a yi ta zancen `yan ta’adda a nan. Gwamnati ce da al’umman Falasɗinawa suka zaɓa. Kuma kuɗin nan na Falasɗinawan ne. Shi ya sa bang a dalilin ƙin sako su ba.“

Tuni dai, don rage dogaro kan ƙasashen yamman, da kuma samun wani sabon tushe na kuɗaɗen shiga, shugaban reshen tsara manufofin ƙungiyar ta Hamas mai cibiya a birnin Damascus na ƙasar Siriya, Khaled Meschaal, ya kai ziyara a birnin Teheran, inda ya nemi taimako daga mahukuntan ƙasar ta Iran. Bayan shawarwarin da ya yi da jami’an gwamnatin a birnin Teheran, Meschaal ya kyautata zaton cewa, Iran za ta taimaka wa Hukumar Falasɗinawan da kuɗaɗe. Ya bayyana wa maneman labarai bayan taron cewa:-

„Muna fatar cewa, wannan ziyarar ta mu za ta sa mu dinga samun taimako daga kafofin Larabawa da na muslmi da kuma na kasa da kasa.“

Ita dai Isra’ilan, a halin yanzu tana bai wa Hamas ɗin zabi ne. Ko ta nemi hanayar ci gaba da karbar taimako daga kasashen Yamma, ko kuma ta juya ga samun taimako daga Iran. Shi dai tsohon jami’in diplomasiyyan Isra’ila Alon Liel, yana gargaɗin Hamas ɗin ne da cewa:-

„Ko ku ci gaba da ta’addancin ko kuma ku kawo karshensa. Idan kuka ci gaba da karbo kudi daga Teheran, to mu kuma za mu dau matakai a kanku ne kamar yadda za mu dauka kan Iran.“