Isra'ila ta ƙaddamar da farmaki a Gaza
March 10, 2012Talla
Isra'ila na ci gaba da luguden wata kan yankin Gaza inda ta hallaka mutane aƙalla mutane 14. Wannan kai farmakin Isra'ila wanda aka fara tun daren jiya ya biyo bayan farmakin rokoki daga mayagan gwagwarmaya dake Gaza. Abinda ya fi tunzura lamarin shine kisan wani jagoran mayaƙan kungiyar PRC, inda ƙungiyar dama Hamas suka yi alƙawarin daukar fansa. Kawo yanzu ana ci gaba da kai farmakin jiragen sama daga bangaren Isra'ila, yayinda su kuwa mayaƙan Falasdinu aka ce sun cilla aƙalla rokoki 90 cikin Isra'ila, inda suka raunata mutane hudu.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Abdullahi Tanko Bala