'Isra'ila ta aikata kisan kare dangi a Gaza'
December 5, 2024Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta zargi gwamnatin Isra'ila da aikata "kisan kare dangi" ga Falasdinawa a zirin Gaza sakamakon yaki da ta rika yi tun watan Oktoban 2023.
A wani sabon rahoto da ta fitar a ranar Alhamis, kungiyar ta ce dukkan sharuddan aikata kisan kare dangi sun cika, ko da yake Isra'ila ta sha musanta wannan zargin.
Kungiyar da ke da cibiya a birnin London na Burtaniya, ta ce ta cimma wannan matsayar ce bayan shafe watanni ta na tsefe bayanan jami'an Isra'ila da kuma al'amuran da ke faruwa.
'Ya kamata a binciki Isra'ila kan zargin kisan kare dangi'
Ta kara da cewa duk abubuwa da ake dubawa na shari'a kafun a ayyana laifin kisan kare dangi yayin rikici da makamai sun tabbata a wannan yakin Isra'ila a Gaza.
Jami'an Isra'ila basu ce komai ba kan wannan rahoton na kungiyar ta Amnesty International.
Isra'ila za ta kare matsayarta a kotun duniya
A taron da aka yi na fayyace abinda ake nufi da kisan kare dangi a shekarar 1948, an bayyana "duk wani yunkuri na shafe wata kasa ko wata kabila ko kungiyar addini daga doron kasa a matsayin kisan kare dangi."