Isra'ila ta bude masallacin birnin Kudus
July 16, 2017Isra'ila ta sake bude masallancin Bailtul Mukaddas na birnin Kudus da ta rufe kwanaki biyun da suka gabata, bayan harin da 'yan bindiga Larabawa suka kai wanda ya salwantar da rayukan su sojojin Isra'ila guda biyu. Sai dai Musulmi sun ki shiga cikin masallancin mai tsarki saboda sabbin matakan tsaro da aka dauka ciki har kyamarori da na'urorin bincika karfe a jikin mutum.
Mahukuntan Isra'ila sun bayyana cewar 'yan sanda sun bi 'yan bindigan har cikin masallaci mai tsarki inda suka kashe maharan uku.Wadanda suka fara shiga cikin masallanci a wannan Lahadin sun ta "Allahu Akbar" duk da cewa a haraba ne suka gudanar da sallar azahar. Rundunar' yan sandan Isra'ila ta nunar da cewar biyu daga cikin kofofi takwas ne aka bude tare da sanya na'urar binciken kwakwaf. Harin na ranar Juma'a ya zo ne makonni kalilan bayan da wata 'yar sandar Isra'ila ta mutu bayan da aka daba mata wuka, sannan bayan harin bindiga da wasu Falasdinawa uku suka kai tsohon birnin da ke gabar yamma da Kogin Jordan.