1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta bude ofishin jakadanci a Bahrain

September 30, 2021

Ministan harkokin wajen Isra'ila  Yair Lapid ya isa kasar Bahrain a wannan Alhamis. Wannan ce ziyarar wani babban jami'in Isra'ila ta farko a Bahrain bayan da kasashen suka gyara alakar diflomasiyyar da ke tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/415l1
Bahrain | Ankunft Jair Lapid am Flughafen Manama
Hoto: Israeli Foreign Ministry/AA/picture alliance

Duk da cewa Bahrain ta jima tana alaka jefi-jefi da Isra'ila, kasar da ke cikin Kasashen Larabawa ta fito fili ta nuna adawa da yadda Isra'ila ke muzgunawa Falasdinawa.


A shekarar da ta gabata ne dai Amirka ta sasanta Kasashen Larabawa ciki har da Bahrain da Isra'ila a karkashin wata yarjejeniya da aka yi wa lakabi da ''Abraham Accords''.


A ziyarar da yake yi yanzu haka a Bahrain, ministan harkokin wajen Isra'ilan zai jagoranci bude ofishin jakadancin Isra'ila a birnin Manama na kasar ta Bahrain.