1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta ce babu gudu babu ja da baya akan shirinta na gine gine

March 26, 2010

Israi'la ta jadada aniyarta ta cigaba da gine gine a yankin yammacin kogin jordan

https://p.dw.com/p/Meh4
Gine gine a yakin yammacin kogin jordanHoto: AP

Gwamnatin ƙasar Isra'ila ta ba da sanarwa cewa babu gudu babu ja da baya a game da shirinta na gina sabbin matsagunan Yahudawa a  gabashin birnin Ƙudus da ta mamaye.

Ƙasar ta Isra'ila ta ba da sanarwa ne daubra da taron wani kwamitin taƙaitace da aka girka a kasar da ke yin zaman nazari na duba taiyin da Amirka ta gabatarma ƙasar ta Israila na sake komawa kan tebrin shawarwari.wani kakakin friministan ƙasar a cikin wata sanarwa da ya bayyana ya ce tsarin Israila na gine gine a yanki yammanci kogin jordan yau shekaru 42 da ake yin shin, kuma ba za a canzashi ba sanan ya ce kwamitin dake yi zaman nazari ko ƙaɗan ba zai ƙetare abinda kasar ta tsaidaba  .