Isra'ila ta daina buɗe wuta a zirin Gaza
March 13, 2012ƙasar Masar ta yi nasarar sulhunta rikicin da ya ɓarke tun kwanaki huɗun da suka gabata a zirin Gaza tsakanin Isra'ila da kuma Palesɗinawa. Tashar telebijin mallakar gwamnatin ta Masar ta bayyana cewar ɓangarorin biyu sun amince su ajiye makamai tun da misalin ƙarfe ɗayan dare na wannan talatar.
A halin yanzu dai ba a jin aman bindigogi a Zirin na Gaza da kuma kudancin ƙasar Isra'ila. Dama dai palesdinawan sun yi alƙawarin daina harba wa bani yahudu rokoki. yayin da ita kuma Isra'ila ta ce za ta daina amfani da jiragen saman yaƙinta domin ci-gaba da kai farmaki akan Falasɗinawa a Zirin Gaza.
Tun da farko dai, ƙungiyar Hamas dake jan ragamar iko a Zirin na Gaza ta yi kira ga sauran ƙasashen yankin da su tsoma baki wajen kawo ƙarshen rikicin, wanda ya ɓarke bayan mutuwar wani shugaban gwagwarmayar ƙwato wa palesɗinawa 'yancinsu,a wani harin da jiragen saman yaƙin Isra'ila suka kai a Zirin Gaza.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu