1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta gama janye sojojinta daga Gaza

September 12, 2005

Tare da bukukuwa da shagulgula Palasdinawa suka bayyana farin cikinsu game da janyewar Isra'ila daga Gaza

https://p.dw.com/p/BvZl
Palasdinawa na murnar janyewar Isra'ila
Palasdinawa na murnar janyewar Isra'ilaHoto: AP

Shugaban kasar Palestinu Mahmoud Abbas ya shaidawa manema labarai cewar yau rana ce ta farin ciki wada al’umman Palestinu ba zasu taba ganin irinta ba nan da karni guda. Jami’an tsaron Palastinu sun shiga murna tare da nuna alamar nasara a daidai lokacin da tankokin yaki da motoci masu sulke ke kann hanyarsu ta ficewa daga matsugunan dake yankin Palasdinawa. Brigadiya Aviv Kochavi yace a yau manzancin ya kammalu kuma mamayar Isra’ila ta tsawon shekaru 38 ta zo karshenta. To sai dai kuma wani abin da ya gurbata yanayin janyewar shi ne kaddarar da ta rutsa da wuraren ibadar yahudawa, lamarin da ka iya bari murna ta koma ciki a game da shirin zaman lafiyar da gwamnatin Amurka ta sa baki aka cimmasa. Matasa yan Palestinu sun shiga cinnawa gidajen ibadan yahudawa wuta a unguwanni 21 domin nuna kiyyaya ga mamayewan da Israila tayi wanda gwamnatin Ariel Sharon ta yi jagorancin kawo karshensa domin a cimma zaman lafiya a wannan yankin. Amma abin da ya harzuka Palestinawa shine bukatar da Isra’ila ta nunar na ganin an ci gaba da kare makomar wuraren ibadan. Shi piraminista Sharon dai ya zama zakaran gwaji a duniya sabili da kwashe mutune dubu 8,500 daga zirin gaza wanda aka kammala a tsakanin awa 24 kacal. Ko da yake Palasdinawan na doki da murnar ganin Isra’ila ta janye daga zirin Gaza, amma a daya bangaren suna tsoron cewar mai yiwuwa piraminista Sharon yayi hakan ne domin ya samu wata dama ta karfafa angizon Yahudawa a yankin gabar kogin yammacin Jordan, inda ake fama da ‚yan kaka-gida sama da dubu 245. Palastinawa sun kara nuna damuwa ganin cewar kasar Israila zata cigaba da tsaron iyakokin sassan biyu bisa manufar tabbatar da tsaron kanta. Palasidinawan dai a zirin Gaza sun shiga shagulgula da bukukuwa da yi wa juna sam barka wasu daga cikinsu suna harbe-harbe a iska, inda wani Bapalasdine mai suna Abdallah Sallah ke cewar, a zamanin baya wannan wani dandali ne mai ban tsoro, amma a yanzu ya wayi gari tamkar wurin ziyara mai ba da kwarin guiwa game da makomar Palasdinawa.

Babban aikin dake gaban shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas shi ne da farko ya tabbatar da doka da oda a tsakanin al’umar Palasdinu, musamman ma masu zazzafan ra’ayi daga cikinsu, wadanda suka ki yarda da a kwance damararsu ta makamai. Domin kuwa Isra’ila ta fito fili ta bayyana cewar zata mayar da martani mai tsananin gaske akan duk wani hari na ta’addancin da za a kai mata, kuma zata dora laifin ne akan mahukuntan Palasdinawa. Dangane da ‚yan adawa da wannan mataki a Isra’ila kuwa, janyewar tamkar mika wuya ne ga Palasdinawa masu zazzafan ra’ayi kuma a ganinsu zirin Gaza wani hakkinsu ne daga Indallahi.