1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An janye dakaru Isra'ila

Suleiman Babayo AMA
July 5, 2023

Gwamnatin Isra'ila ta dauki matakin janye dakaru daga yankin gabar yamma da kogin Jodan bayan kakkabe tsageru masu dauke da makamai da suke yi mata barazana.

https://p.dw.com/p/4TS6E
yankin gabar yamma da kogin Jodan | Lokacin samamen dakarun Isra'ila
Yankin gabar yamma da kogin JodanHoto: Jaafar Ashtiyeh/AFP/Getty Images

Gwamnatin kasar Isra'ila ta janye dakaru daga yankin gabar yamma da kogin Jodan inda tsageru masu dauke da makamai suka yi kaka-gida, abin da ya kawo karshen matakin soja na tsawon kwanaki biyu da ya yi sanadiyar mutuwar Falasdinawa kimanin 12.

Sojojin sun bayyana samun galaba wajen yin ta'adi kan tsagerun yayin samame a sansanin 'yan gudun hijira na Jenin. Akwai sojan Isra'ila daya da ya rasa ransa lokacin artabun.

Gabanin janye dakarun Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ya sha alwashin cewa za a sake amfanin da sojojin muddun aka sake samun barazana daga kungiyoyin tsageru masu dauke da makamai na Falasdinu.