Isra'ila ta kai hare-hare a Zirin Gaza
August 4, 2014Talla
An kai harin ne da makamai masu linzami da jiragen sama na yaƙi a kan wata cibiya ta 'yan gudun hijira da ke a yammancin Gaza a Chati. Wannan mutumin wani mazaunin unguwar ce ta Chati.
''Sun kashe iyalai da dama ,wani wurin dukkanini yalen gidan, an kashesu wannan rashin hankali ne, kuma ba za mu amince da shi ba.''
Ƙungiyar Hamas da Isra'ilan na zargin junansu da karya yarjeniyar. Tun farko gwamnatin Isra'ilan ta ce yarjejeniyar ba ta shafi yankin kudanci ba na Rafa.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe