1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta kai hare-hare kan Hamas

Mahmud Yaya Azare
December 8, 2017

Ana yin mummunan artabu tsakanin Falasdinawan da ke adawa da mayar da birnin Kudus fadar mulkin Isra'ila da jami'an tsaron Isra'ilan a yayin da jiragen sama na yaki na Isra'ila suka kai hari kan kungiyar Hamas.

https://p.dw.com/p/2p2XJ
Syrien Aleppo Raketenangriff
Hoto: picture-alliance/AP Photo/A. Hüseyin

Artabun dai anan yin sa ne tsakanin Falasdinawan dake fusace da matakin halastawa Isra'ila birnin Kudus da Amurka tayi, da kuma sojoji da jami,an tsaron Isra,ila, wadanda sukai ta harba  barkwanan tsohuwa da harsashin roba dama mai kisa, yadda a kalla, a ka raunata mutane akalla dubu daya.

Wannan sabon boren dai, da aka gudanar da shi a garuruwan Ramallah da Al-khalel da Ariha Nablus dama yankin Gaza, somin-tabi ne a boren sai Baba-ta-gani da Falasdinawan ke kiransa Intifada, da zimmar tirsasawa Amirka janye matakin mai da birnin Kudus fadar mulkin Isra'ila da ta yi, inji shugaban kungiyar Hamas a Gaza, Ismail Haniyeh wanda ya kira wannan sabuwar fafutukar da Intifada ta uku.

“Yau rana ce ta fushi da za mu sanya dan ba, a sabuwar gwagwarmayar boren Intifada a karo na uku, don lalata mugun tanadin mallake birnin Kudus, ga haramtacciyar kasar Isra'ila da Amirka ta yi, don kuma lalata yarjejeniyar Oslo, wacca ta dankusar da Falasdinawa, ta kuma rabasu da babban makaminsu na tayar da kayar baya. Ina kira da a shirya don tunkarar duk abun da zai kai ya komo.”

Wata tsohuwa da ta ci-gaba da dannawa, duk da kasa ganin da ta yi sakamakon hahharba hayaki mai sa kwalla, ta ce ba gudu ba ja da baya kan wannan gwagwarmayar:

Syrien Aleppo Zerstörung Raketenangriff
Hoto: Reuters/A. Ismail

  “Tawadar da aka rubuta wannan matakin na kyauta da kayan wani da aka sata, ta fi shi kansa matakin kima. Aikin banza Amirka ta yi. Domin babu abun da za mu bari ya canja a kasa. Muna nan daram a cikn kasarmu. Za kuma mu ci-gaba da kalubalantarsu ko da mu kadai ne.”

Ita kuwa Kungiyar Jihadul Islami mai gwagwarmaya da makamai, kira ta yi ga hukumar Falalsdinawa da ta ayyana kawo karshen shirin tattaunawar zaman lafiya da Isra,ila:

“Muna kira da a futo a shelanta lalacewar yunkurin shirin sasantawar da ake da Isra'ila. A kuma kawo karshen aiki da yarjejeniyar Oslo. Da kuma aikin kafada–da –kafadar da hukumar Falalsdinawa ke yi kan lamuran tsaro da makiyiyarmu  Isra'ila.”

Wannan zanga-zangar nuna fushin dai ba ta tsaya kan Isra'ila da Amirka kadai ba, ta hada har da kan shuwagabannin Larabawan da Falasdinawan da ake zarginsu da hade musu baki.