Isra'ila ta kai harin martani a Zirin Gaza
August 19, 2014Mayakan sa kai sun harba makaman roka uku zuwa Isra'ila inda suka fada kudancin birnin Beersheva. Wasu bayanai da ke fitowa daga majiyar sojan na Isra'ila sun bayyana cewa harin na zuwa ne gabannin sa'o'i da aka sake warewa na karin wa'adin lokacin tsagaita bude wuta tsakanin bangarorin biyu da ke gaba da juna.
Mai magana da yawun sojan na Isra'ila ta fada wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa makaman sun fada ne wasu filaye a birnin na Beersheva. Sai dai babu asarar rayuka da aka samu.Tuni dai Firaminista Benjamin Netanyahu ya bada umarnin maida martani kan wannan hari.
Wakilin kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce ya ga lokacin da jirgin yaki na Isra'ila ke harba makamai masu linzami a gabashin birnin na Gaza, harin da majiyar sojan ke cewa ya na da nufin samun 'yan ta'adda a yankin.
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Muhammadou Awal Balarabe