1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta kai hari kan Hamas a Gaza

Gazali Abdou Tasawa
November 16, 2019

Sojojin Isra'ila sun sanar da kaddamar da sabbin hare-hare tun da sahin safiyar wannan Asabar a ziri Gaza a matsayin martani ga wasu sabbin hare-haren rokoki da Isra'ilar ta fuskanta daga mayakan Palasdinawa.

https://p.dw.com/p/3T9T6
Gazastreifen Khan Yunis | Israelischer Luftangriff
Hoto: Getty Images/AFP/A. Rahim Khatib

Sojojin Isra'ila sun sanar da kaddamar da sabbin hare-hare tun da sahin safiyar wannan Asabar a ziri Gaza a matsayin martani ga wasu sabbin hare-haren rokoki da Isra'ilar ta fuskanta daga mayakan Palasdinawa wannan kuwa duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da bangarorin biyu suka cimma yau da kwanaki biyu.

 Sai dai kamfanin dillancin Labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa rundunar sojojin Isra'ilar ta kai sabbin hare-haren ne a kan mayakan Kungiyar Hamas mai rike da iko da yankin na Gaza da wacce ba ta shiga fadan da ake yi ba tun bayan barkewarsa a farkon wannan mako.Rundunar sojojin Isra'ilar ta ce ta yi nasarar kakkabo rokokin da aka harbo cikin kasar daga zirin na Gaza.

 Palasdinawa 34 ne dai suka halaka a zirin na Gaza a kwanaki biyu na farkon barkewar rikicin, a yayin da mayakan Kungiyar ta Jihad islamique suka harba rokoki 450 zuwa cikin kasar ta isra'ila kafin bangarorin biyu su amince tsagaita wuta a ranar Alhamis da ta gabata.