1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Isra'ila ta kai sabbin hare-hare a Zirin Gaza

October 22, 2023

Hamas ta ce, kimanin mutane 55 ne suka mutu a a hare-haren da Isra'ila ta kai yankin bayan da Isra'ilar ta ce za ta kara lugaden wuta a Gaza.

https://p.dw.com/p/4Xrkp
Hoto: Said Khatib/AFP

Gwamnatin Hamas ta sanar da cewa, kimanin mutane 55 ne suka mutu a hare-haren da Isra'ila ta kai Gaza. Hamas din ta kuma ce, fiye da gidaje 30 ne suka lalace a hare-haren na cikin dare. Hakan dai na zuwa ne bayan da rundunar sojin Isra'ila ta ce ta na shirin kara zafafa kai hare-hare ta sama kan Hamas a zirin Gaza.

Karin bayani: Masar ta shirya taron zaman lafiya kan rikicin Gaza

Kakakin rundunar, Daniel Hagari ya ce, shirin fara lugaden wutan wani mataki ne gaba a yakin da suke yi da Hamas kana su rage hadarin da dakarunsu suke fuskanta. Tuni dai Isra'ila ta bada umurnin ga mazauna arewacin Gaza da su fice daga yankin zuwa kudanci domin tsiratar da rayuwarsu.

Isra'ila ta ce kimanin mutane dubu 700 ne suka bar yankunansu zuwa kudancin Gaza yayin da yankin ke ci gaba fuskantar karancin ruwa da abinci da kuma wutar lantarki.