1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta kai sabon hari a Gaza

August 14, 2014

Duk da batun cimma sabon wa'adin tsagaita wuta na kwanaki biyar a rikicin da ake tsakanin Isra'ila da Hamas, jiragen yakin Isra'ila sun kai hari a arewacin Gaza.

https://p.dw.com/p/1CuV8
Israelische Soldaten Nahostkonflikt 13.8.2014
Hoto: Reuters

Rahotanni daga yankin Zirin Gaza na Falasdinu, sun tabbatar cewa jiragen yakin Isra'ila sun yi ruwan bama-bama a yankin arewacin Gaza, a cewar wadanda suka gane ma idanun su, da ma 'yan kungiyar Hamas: Hakan ya faru ne duk kuwa da cewa, an sanar da batun kara wa'adin tsagaita wutar da ya kare a ranar Laraba ya zuwa kwanaki biyar nan gaba daga wannan Alhamis. Sai dai ana ganin cewa da alama babu wadanda suka rasu cikin wannan sabon harin na Isra'ila.

Firaministan Isra'ila Benjamin Nethanyahu ne ya bai wa rundunar sojan kasar izinin kai wannan hari a matsayin mayar da martani kan wata roka da aka harba a cewar su daga yankin na arewacin Zirin na Gaza 'yan mintoci kalilan kafin lokacin cikar wa'adin tsagaita wutar, zargin da kungiyar Hamas ta karyata.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu