An kama wanda ya harbe mutane a Isra'ila
August 14, 2022Talla
'Yan sandan Isra'ila sun kama mutumnin da ya bude wuta kan wata motar bas a kusa da wurin ibadar Yahudawa a ranar Asabar, inda ya jikkata akalla mutane bakwai.
"An kawo mutane 6 da suka ji rauni a sashinmu, biyu na cikin mummunan yanayi - akwai mace mai ciki da ta ji rauni haryanzu tana dakin tiyawa. da wani mutum mai shekaru 60 da ya samu rauni a wuyansa da kai, wasu mutane hudu na fama da rauni a kirji da gabobin jikinsu." inji wani daraktan rukunin taimakon gaggawa a cibiyar kiwon lafiya ta Shaare Zedek.
Harin dai na zuwa ne mako guda bayan kazamin fada na tsawon kwanaki uku tsakanin Isra'ila da 'yan faftukar jihadi a yankin zirin Gaza, an kiyasta mutuwar mutane 49, kasar Masar ce ta jagoranci shiga sulhu don samun zaman lafiya.