Isra'ila ta kashe wasu kwamandojin Hamas
August 21, 2014Talla
A wani sako da Hamas din ta fidda, ta ce mutanen da suka hada da Mohammed Abu Shammala da Raed al-Attar da kuma Mohammed Barhoum sun rasa ransu ne bayan da aka kai farmaki kan wani gini da suke ciki a kudancin Rafah.
Kisan wadannan kwamandojin dai na zuwa ne bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi tsakanin Hamas din da Isra'ila ta rushe, batun da ya sanya kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da sauran kasashe cigaba da nuna damuwa dangane da yanayin da ake ciki.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Ummaru Aliyu