Isra'ila ta rufe filin jirgin samanta dake kan iyaka da Masar saboda dalilan tsaro
August 8, 2013Mahukuntan Isra'ila sun rufe filin jirgin saman Eilat dake kudancin kasar, kusa da yankin tsibirin Sinai na kasar Masar saboda dalilai na tsaro. Wata mai magana da yawon rundunar sojin Isra'ila ta ce bayan wani nazari a kan tsaro, rundunar sojin Isra'ila ta ba da umarni a soke sauka da tashin jiragen sama a filin jirgin saman na Eilat dake kan iyaka da Masar. Sai dai ba ta yi karin bayani ba. Masu yawan shakatawa na amfani da filin jirgin saman birnin dake Tekun Bahar Maliya, don zuwa wurin shakatawa na Eilat. Rufe shi na da nasaba da karuwar aikace-aikacen masu kishin addinin Islama a Sinai dake makwabtaka. A watan da ya gabata Isra'ila ta karfafa matakan kariya daga harin rokoki kusa da kan iyakarta ta kudu don dakile duk wasu hare-hare da za a iya kai wa kasar ta Yuhudu. A halin yanzu an sake bude filin jirgin saman.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman