Isra'ila ta sako fursunonin Falasɗinu
August 14, 2013Talla
Jagoran Falasɗinawa wanda shi ne ya tarbesu a Ramallah Mahamud Abbas ya ce wannan wata rana ce ta farin ciki, sannan ya ƙara da cewar : Ya ce: '' Wannan kishi na farko kennan, kuma za mu ci gaba da yin gwagwarmaya har sai a sako dukkanin magoya baya mu da ake tsare da su.''
Isra'ila ta sako fursunoni 26 waɗanda ke cikin rukunin na fursuna 104 da za a sako a nan gaba. Yau da yamma aka shirya za a soma yin zagaye na biyu na tattaunawa sake farfaɗo da shirin zaman lafiya, tsakanin Yahudawan da Larabawan Falasɗinu bayan da shirin ya cije sama da watanni tara a yankin na Gabas ta Tsakiya.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu