Isra'ila ta soki manyan kasashen Duniya
May 16, 2018Talla
Wannan jan hankali da Ministan yayi ya biyo bayan wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Tweeter inda ya bayyana kasashen da suke sukar matakin da Isra'ilan ke dauka akan Falasdinawa da cewa Munafukai ne.
A nata bangaren Kungiyar Hamas ta Falasdinawa ta bayyana cewar ya zuwa yanzu akalla Falasdinawa fiye da sittin ne suka rasa rayukan su yayin arangama tsakanin su da Sojojin Isra'ila a ranar litinin din da ta gabata.
A wani cigaban kuma shugaban kasar Rasha Vlamir Putin da takwaransa na kasar Turkiyya sun yi Allah wadai da harin da Isra'ila ke cigaba da kai wa yankin Gaza.