1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta yi sassauci a masallacin Kudus

Gazali Abdou TasawaOctober 23, 2015

Isra'ila ta bai wa Musulmi Palasdinawa izinin shiga masallacin Kudus ba tare da gitta wani sharadi ba, a wani mataki na kashe wutar rikicin da ya taso tsakanin sassa biyu.

https://p.dw.com/p/1GtH2
Israel Zusammenstöße in Jerusalem Polizisten auf dem Dach der Al Aksa Moschee
Hoto: Reuters/B. Ratner

Hukumomin kasar Isra'ila sun bada sanarwar yin sassuci ga matakan takaita shiga masallacin birnin Kudus a wani mataki na neman kashe wutar rikicin da ake fama da shi yau da 'yan makonni tsakanin Palasdinawan da Isra'ilar.

A karkashin matakin sassucin dai, tun a wannan Jumma'a hukumomin Isra'ilar sun bai wa illahirin musulmin Palasdinawan izinin halartar sallar Jumma'a a masallacin mai tsarki ba tare da gitta wani sharadi ba. A baya dai Isra'ilar ta haramta wa musulmin da ba su kai shekaru 50 ba izinin shiga masallacin.

Mutane 57 ne dai suka mutu daga ciki Palasdinawa 49 tun bayan barkewar wannan sabon rikici tsakanin Isra'ilar da Falasdinwan a farkon wannan wata na Oktoba