Fadada matsugunan Yahudawa
July 27, 2018Talla
Isra'ila ta bayyana aniya ta sake gina sabbin matsugunan Yahudawa daruruwa a yammacin kogin Jodan, matakin da ke zuwa bayan da wani Bafalasdine ya halaka Bayahude guda da raunata wasu uku. Ministan harkokin tsaron Isra'ila Avigdor Lieberman ya bayyana haka a wannan rana ta Juma'a.
"Amsa mafi kyau a yaki da ta'addanci shi ne fadada matsunan Yahudawa" bayanin kenan da Lieberman ya wallafa a shafinsa na Twitter. Ya ce za su gina gidaje 400 a yankin Adam da ke a arewacin Birnin Kudus. Wani matashi dai Bafalasdine ya tsallaka shinge inda afka yankin da Yahudawan suke zaune ya rika daba masu wuka, lamarin da ya yi sanadin rai na guda daya sauran ukun kuwa suka sami raunika.