Isra'ila za ta gina karin matsugunai
October 24, 2021Talla
Sanarwar da ministan gine-gine da gidaje na kasar ya fitar na cewa za a gina sabbin gidajen ne a matsugunnai bakwai, inda za a gina kimanin gidaje 729 a garin Ariel da ke arewacin gabar kogin.
A halin yanzu dai fiye da Yahudawan kama wuri zauna dubu hudu ne suka mamaye gabar kogin da Falasdinawa ke ikaririn yankinsu ne. Sai dai kuma dokar kasa da kasa ta ayyana matsugunni a matsayin haramtacce.
Falasdiwa dake fafutukar kafa kasarsu a gabar kogin na ganin kara gina gidajen a matsayin abun da zai kawo cikas ga fatan samun zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu. Isara'ila dai na ikrarin cikakken iko da gabar yamma ta kogin Jordan, inda Falasdiwa kimanin miliyan 2 ke zaune tun bayan yakin kwanaki 6 a shekarar 1967.