Isra'ila za ta kori baƙin haure
August 31, 2013Talla
A lokacin da ya zanta da manema labarai a kan wannan batu ministan cikin gidan isra'ila ya nunar da cewar a watan Oktoba ne za a fara tisa ƙeyar baƙin ba tare da bayyana ƙasar da za ta karɓe su ba. Kimanin baƙin haure dubu hamsin ne waɗanda galibinsu suka fito daga ƙasashen Sudan da sauran ƙasahe ke zauna a Isra'ila.
Gwamnatin Benjamin Netanyahu za ta bai wa duk wanda za a fitar daga ƙasar kimanin Euro dubu da ɗari biyar don su riƙe a hannunsu. Sai dai kuma ta yi barazanar ɗaukan matakan rashin sani da sabo daga bisani kan duk baƙin da za su ci gaba da zama a ƙasar ba bisa ƙa'ida ba.
Mawallafi : Mouhamadou Awal Balarabe
Edita : Abdourahamane Hassane