Isra'ila za ta mayar da 'yan gudun hijrar Afirka gida
April 13, 2018Talla
Wakilan kasashen biyu sun shiga wata tattaunawa domin cimma matsaya kan batun yin na'am da bukatar amsar 'yan gudun hijrar, da yanzu haka ke zaune a Israila domin a basu mafaka a kasar ta Yuganda.
Wannan na zuwa ne bayan da a watan Janairun wannan shekara ta 2018 da muke ciki, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ba wa 'yan gudun hijira mafi akasari wadanda suka fito daga kasashen Afirka zuwa Isra'ila ba bisa ka'ida ba zabin fita daga kasar cikin girma da arziki ko da karfin tuwo, matakin da ya fuskanci suka daga hukumomin kare hakin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin fararen hula da ke rajin kare hakkin dan Adam din a duniya.