1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila za ta yi musayar bayanai da Saudiyya

Yusuf Bala Nayaya
November 16, 2017

Janar Gadi Eizenkot ya kuma fadawa kafar yada labaran mai zaman kanta mai tushe da Saudiyya Elaph ba su da shiri na kai hari ga Hezbollah.

https://p.dw.com/p/2nlvK
Israel IDF Armee Generalstabschef Gadi Eisenkot
Janar Gadi EizenkotHoto: imago

Shugaban sojoji a Isra'ila ya bayyana wa wata kafar yada labarai ta Larabawa da ke watsa labaranta a shafin intanet cewa Isra'ila a shirye ta ke ta yi musayar bayanan sirri da kasar Saudiyya kasancewar kasashen biyu a shirye suke kan duk wani abu da zai sa su yi gaba da gaba da Iran.

Janar Gadi Eizenkot ya kuma fadawa kafar yada labaran mai zaman kanta mai tushe da Saudiyya Elaph a zantawarsa ta farko da wata kafar yada labarai mai watsa shiri a harshen Larabci cewa  Isra'ila ba ta da wani shiri na kai farmaki ga mayakan Hezbollah da ke a Lebanon.

Kasar Saudiyya dai a baya-bayan nan na ci gaba da nuna yatsa ga Iran wacce take zargin mahukuntanta na Tehran da kokari na fadada iko a kasashen Larabawa ciki kuwa har da amfani da 'yan Hezbollah da ke zama 'yan Shi'a a kasar Lebanon.