Isra'ilawa na faman ji da hare-haren Hamas
Hare-haren ta'addancin Hamas ya bai wa Isra'ila mamaki. Baya ga kashe-kashen da suka yi, hare-haren sun kuma nuna kasawar jami'an tsaron Isra'ila.
Bikin kade-kade ya rikide na makoki
Daya daga cikin munanan hare-hare da Hamas ta kai, shi ne kan bikin kade-kade na Supernova, wanda aka gudanar a wajen shakatawa da ke kusa da Gaza. Ya kasance wuri mai sauki yayin da mayakan Hamas suka kutsa kai kan iyakar. Masu halartar bikin sun gudu a firgice. Akalla mutum 260 ba su tsira ba, yayin da wasu kuma aka yi garkuwa da su. Sojojin Isra'ila da aka gani a nan, daga baya sun tsare wurin.
Fatattakar Hamas
Sojojin Isra'ila na shiga yankunan Falasdinawa akai-akai domin gudanar da samamai da kan kashe mayaka da fararen hula. Sau tari hakan na faruwa fiye da samamai a cikin gida. Da alama hukumomi ba su da shiri don kare garuruwan Isra'ila da ke kusa da Gaza wadanda mayakan Hamas ke kai wa hari. Sojoji sun yi nisa a fatattakar mayakan, kamar wanda aka gani, amma kuma an riga an yi barna.
Jana'iza a Isra'ila
Rikicin Isra'ila da Hamas kan haifar da asarar rayuka a bangaren Falasdinawa. Amma a farmakin ba-zata kan Isra'ila, hare-haren Hamas sun fin yin barna a farkon fari. Kusan yawancin yan Isra'ila, akasari fararen hula, an kashe su a karshen mako kamar kisan intifada na 2 a farkon shekarun 2000. Dokar addinin Yahudawa na bukatar gaggauta binne mutane, don haka an yi jana'izar jim kadan bayan harin.
Agajin farko
Wasu Yahudawan Isra'ila masu addini za a iya kebe su daga aikin soja na dole. Su na samun hanyoyin da ba na soja ba don ba da gudummawa, kamar gudummawar jini. A cikin sa'o'i na kutsen Hamas, asibitoci sun fuskanci dubban mutane da suka jikkata. A Gaza, saboda kangewar da Isra'ila ta yi, kayayyakin jinya basu da wani katabus da za su yi a farmakin Isra'ila kan yakin na Gaza.
Nisan tasirin rikicin
Sabon yakin Isra'ila da Hamas ya na da sakamako ga duniya, ba kawai dangane da siyasar yankin ba. Tare da hani kan Falasdinawa da ke shiga Isra'ila don yin aiki, yawancin ayyukan wucin gadi da karancin albashi baki yan ci-rani ke yinsu. Dubban mutanen Thailand ne ke zaune a Isra'ila, kuma wasunsu na cikin wadanda mayakan Hamas suka kashe ko kuma suka yi garkuwa da su, wasu kuma ba labarinsu.
Babbar manufar tsaron Isra'ila
Yayin da suke fama da dimuwa, yawancin 'yan Isra'ila suna tambayar yadda Hamas ta kaddamar da harin ba tare da gargadi ba. Wasu rahotannin kafafen yada labarai da kungiyoyin kare hakkin bil'adama na Isra'ila, sun nunar da cewa Isra'ila ta karkatar da kudinta wajen 'yan share wuri zauna da ke cikin yankunan Falasdinawa da aka mamaye a yammacin gabar kogin Jordan a maimakon kare 'yan kasarta.
Shirya wa yaki
Sojojin Isra'ila, ba sa hutawa da bakin ciki. Za a iya ba wa dubbai umarnin shiga Gaza, wacce Isra'ila ta bari a hukumance tun 2005 yayin da take iko da zirga-zirgar sama da ta teku da ta kasa. Gabanin yiwuwar kutsen, Firaministan Isra'ila Netanyahu ya umarci 'yan Gaza su fice, abin da ke da matukar wuya bayan rufe daukacin yakin Gaza daga kan iyakarsu da Isra'ila da kuma ta kasar Masar.