1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iƙirarin Isra'ila na fuskantar hari

Halimatu AbbasAugust 2, 2010

Israi'la ta yi iƙirarin fuskantar harin roka daga Masar

https://p.dw.com/p/OZkz
Mayaƙin Falisɗinu ɗauke da rokaHoto: picture-alliance/dpa

Hukumomin Isra'ila sun sanar da cewar, aƙalla makaman roka ukku ne suka faɗa a yankin Eilat da safiyar yau Litinin, amma ba tare da raunata ko da mutum guda ba. Suka ce sun yi amannar cewar, rokoki biyar ne aka jefa, amma ɗaya ya faɗa a yankin tashar jiragen ruwar Jordan, wanda kuma ya raunata mutane huɗu inda suka ce mai yiwuwa daga Masar ne aka jefa rokokoin. A halin da ake ciki kuma, aƙalla Falasɗinawa 15 suka sami rauni bayan tarwatsewar wani abu a gidan wani kwamandan mayaƙan Hamas na Falasɗinu a zirin Gaza. Falasɗinawa dai sun bayyana cewar, wani harin da Isra'ila ta ƙaddamar ta jiragen sama ne ya janyo tarwatsewar bam, amma ita Isra'ila ta ƙaryata hakan.

Jami'an Falasɗinawa suka ce harin, wanda aka ƙaddamar da safiyar wannan Litinin, ya lalata gidan wani kwamandan mayaƙan Hamas, Ala Adnaf. Rahotannin da ba a tabbatar da sahihancinsu ba sun ruwaito cewar, mutane biyu ne suka mutu a sanadiyyar harin. Tun da farko dai, Firaministan Isra'ila Benjamin Natanyahu ya gargaɗi shugabannin zirin Gaza, wanda ke ƙarƙashin ƙungiyar Hamas, bayan da wani harin makamin rokar da ake zargi ya fito ne daga yankin, ya sauka a wani gidan da ke yankin Isra'ila. A ƙarshen mako ne dai aka kai harin na makamin roka, wanda ko da shike bai faɗa kan kowa ba, amma ya lalata wani gida.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Halima Balaraba Abbas