Zuma ya samu izinin barin gidan kaso
July 22, 2021Talla
An yanke wa mai shekaru 79 da haihuwar, hukuncin zaman gidan yari na watanni 15 a watan da ya gabata, bayan kaucewa masu binciken almundahana da aka yi lokacin shugabancinsa.
A ranar 8 ga watan Julin nan ne dai ya mika kansa domin fara wa'adin zaman gidan kurkukun a garin Estcourt da ke yankin Kudu maso Gabashin kasar. Kwanaki bayan nan ne kaninsa mai shekaru 77 ya mutu.
Hukuncin da kotun Afirka ta kudun ta yanke masa dai, ya janyo zanga zanga da tarzoma da dibar ganima da ba a taba ganin irinsa ba tun bayan da aka kawo karshen zamanin nuna wariyar lauinin fata na Apatheid. Rikicin kuma da ya yi sanadiyyar rayukan mutanen 276.