Jama'ar Diffa na murna da dokar ta-baci
February 25, 2015
Hakikan a yayin da dokar ta-bacin ta tsawon makwonni biyu ke daf da kawo karshent, a tun bayan hare-haren ta'addanci da tashin bama -baman da al'ummar birnin na Diffa suka tsinci kansu, tare da kaurace ma muhallan su ciki. Saffi da matasa masu ji a jika da ke zama a birnin na Diffa ne dai suka bayyana gamsuwarsu da dokar da aka kafa.
Matakin karshe da mazauna a birnin na Diffa da kewaye dai suka dauka, shi na fatan ganin hukumomin koli na kasar ba ma na jihar ta Diffa ba, wato majalisar dokoki ta gaggauta ayyana makamanciyar wanan doka.
Rohotanni daga jihar ta Diffa dai na cewar jami'an tsaro sun kama mutanen da ke zato sune da alhakin dasa nakiyoyi a karamar hukumar Bosso, wacce ta yi
sanadiyar mutuwar jami'an tsaron kasar guda biyu, tare kuma da jikata wasu.