Nijar ta rufe wuraren hakar Gwal mallakin kasar Chaina
May 5, 2024Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun bada umarnin rufe wasu wuraren hakar Gwal guda hudu na kasar da ke karkashin kamfanin kasar Chaina, bayan mutuwar dabbobi masu tarin yawa da suka sha gurbataccen ruwan dagwalon da ke fitowa daga kamfanin.
Karin bayani:Nijar ta ciyo bashin kudi daga Chaina
Ma'aikatar kula da ma'adanan kasar ce dai ta bada umarnin rufe kamfanin na kasar Chaina mai suna Sahara SARL, bayan ziyarar gani da ido, bisa rakiyar jami'an 'yan sanda da ke binciken lamarin.
Karin bayani:Chaina za ta ci gaba da ayyukanta a Nijar
Tun a cikin watan Janairun da ya gabata ne dai kamfanin ya fara aikin hakar Gwal a yankin.
Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun jima suna kokawa da yadda kamfanin hakar Uranium na Faransa Orano da ake kira Areva a da ke gurbata muhalli a kasar, bayan ya shafe shekaru sama da 40 yana aikin hakar ma'adanan a arewacin Jamhuriyar Nijar.