1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an diflomasiya na taro a Paris kan mayakan IS

September 15, 2014

Amirkan tana iya sake tunani wajen tura dakaru baya ga kayan yaki da ba da horo da kai farmakin yaki ta sama kan mayakan IS

https://p.dw.com/p/1DCFJ
Der irakische Präsident Fouad Massoum trifft am Flughafen in Paris am Vortag der Konferenz ein 14.09.2014
Hoto: picture alliance/AP Photo/Francois Mori

Bayan sake kisan wani jami'i daga yammacin duniya da mayakan IS suka yi, jamian diflomasiya daga sassa daban-daban na duniya sun tattaru a birnin Paris inda suke bukatar samar da wani shiri na duniya da zai kawo karshen mayakan masu kaifin kishin Islama na kungiyar IS, sai dai babu wata tawaga daga bangaren kasashe biyu da suke da muhimmiyar rawa da za su taka a wannan rikici da ke neman fantsama zuwa wasu kasashe baya ga yankin na gabas ta tsakiya.

Kasashe kuwa irin su Iran sun bayyana rashin goyon bayansu ga wannan shiri na yakar kungiyar ta IS.

A ranar Lahadi fadar ta White House ta bayyana cewa tana neman kawaye da za su ba da gudumawar dakarun soji, abin da ba a tsammani daga bangaren na Amirka, sai dai ita Amirka tuni ta kaddamar da hari kan mayakan ta hanyar amfani da jiragen sama na yaki.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo