1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an EU na ziyara a kasar Zimbabuwe

Salissou Boukari
March 19, 2018

Tawagar Kungiyar Tarayyar Turai ta soma wata ziyara daga wannan Litinin din a kasar Zimbabuwe, a wani mataki na shirin tura masu sa idanu a kan zabukan kasar da za su gudana a watan Yuli mai zuwa.

https://p.dw.com/p/2uaKQ
Davos WEF Emmerson Mnangagwa zu Wahlen  Simbabwe
Hoto: Getty Images/AFP/F. Coffrini

Zabukan su ne za su kasance na farko tun bayan kifar da shugaban kasar Robert Mugabe daga shugabancin kasar. Rabon dai kungiyar Tarayyar Turai ta kai irin wannan ziyara a kasar ta Zimbabuwe, tun a zabukan kasar na 2002 wanda ya bai wa Shugaba Mugabe nasara, amma aka yi ta cece-kuce kan zargin tafka magudi.

A halin yanzu dai sabon shugaban kasar ta Zimbabuwe ne Emmerson Mnangagwa, ya gayyaci kungiyar ta Tarayyar Turai da ta aiko da masu sa idanu a lokacin zabukan kasar masu zuwa, kuma burin na wannan ziyarar shi ne na duba yadda tsare-tsaren zabukan ke gudana a cewar Tarayyar Turai. Mambobin tawagar dai za su gana da hukumar zaben kasar, sannan su mika shawarwarinsu ga hukumar Tarayyar Turai kafin aikewa da masu sa idanu ga zabukan na Zimbabuwe.