Afganistan: Jami'an tsaro 100 sun halaka
August 13, 2018Talla
Akalla jami'an tsaro 100 ne suka halaka a fadan da ake fafatawa da mayakan Taliban a kokarin korarsu daga birnin Ghazni na Afganistan, ministan gwamnati ya bayyana haka a wannan rana ta Litinin bayan kwanaki hudu ana fafata yaki.
A cewar ministan tsaro na Afganistan Tariq Shah Bahrami jami'an tsaro kimanin 100 sun halaka, akwai kuma fararen hula kimanin 20 zuwa 30 wadanda suma sun halaka a wannan fafatawa da aka yi da mayakan na Taliban tsawon kwanakin hudu.