SiyasaJamus
Jami'an tsaro sun sake afka wa 'yan Sudan
January 6, 2022Talla
Jami'an tsaro a Sudan, sun afka wa dubban masu zanga-zangar da ke neman a dawo da kasar bisa turbar dimukuradiyya a wannan Alhamis
Rahotanni na cewa jami'an na tsaro sun kashe akalla mutum guda, bayan harbi da suka yi masa a ka.
Da farko dai hukumomin na Sudan sun datse hanyoyin sadarwa ciki har da na Intanet a kokarinsu na rage hanzarin shirye-shiryen da masu zanga-zangar adawa da gwamnatin.
Haka nan ma hukumomin sun toshe wasu manyan gadoji da ke Khartoum babban birnin kasar, da ma wasu da ke a biranen Bahri da Omdurman.
Sai dai masu zangar-zangar sun lashi takobin isa fadar shugaban kasa da ke a birnin Khartoum, a ci gaba da matsa wa mahukuntan sojin lamba.