CDU za ta zabi sabon shugaba
February 24, 2020Talla
A yau ne ake sa ran jam'iyyar CDU ta 'yan mazan jiya a Jamus za ta bayyana sabon shugabanta bayan rudanin da jam'iyyar ta shiga a baya kan wanda zai gaji Shugabar gwamnati Angela Merkel da ke shirin barin mulki a 2022.
Ana sa ran a wannan litinin tsohuwar shugabar jam'iyyar Annegret Kramp-Karrenbauer za ta bayyana matsayarta bayan yin murabus daga shugabacin jam'iyyar a watan Janairu.