1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Donald Turmp zai yi wa Republican takara

Abdourahamane Hassane
August 24, 2020

Jam'iyyar Republican ta kaddamar da Donald Trump a matsayin dan takarar ta a hukumance a zaben shugaban kasa na uku ga watan Nuwamba da za ayi a Amirka.

https://p.dw.com/p/3hRF4
USA Wahlkampf Präsident Donald Trump
Hoto: Getty Images/AFP/C. Carlson

Wakilan jam'iyyar kusan 300 daga jihohi guda 50 suka amince wakilta Donald Trump din a zaben shugaban kasa a wa'adi na biyu a taron da suka yi a  Carolina ta yamma. Donald Trump ya sha alwashin canza hasashen alkalluma da ake bayyanawa kafin zaben wanda ke nuna cewar dan takarar jam'iyyar Democrats Joe Biden shi ne zai yi nasara a zaben.