1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar Zanu PF ta raba gari da shugaba Mugabe

Gazali Abdou Tasawa
November 19, 2017

A kasar zimbabuwe jam'iyyar Zanu PF mai mulki ta tsige Shugaba Mugabe daga mukaminsa na shugaban jam'iyyar tare da maye gurbinsa da tsohon mataimakinsa Emmerson Mnangagwa.

https://p.dw.com/p/2nt9T
Emmerson Mnangagwa und Robert Mugabe in Simbabwe
Hoto: picture alliance/dpa/AP Photo/T. Mukwazhi

A kasar zimbabuwe jam'iyyar Zanu PF mai mulki ta Shugaba Mugabe ta dauki wannan mataki a wani taro da ta gudanar a wannan Lahadi domin bayyana matsayinta kan makomar shugaban kasar.

 Dama dai tun da sanhin safiyar wannan Lahadi kungiyar matasan jam'iyyar ta fitar da tata sanarwa inda ta bayyana bukatar korar matar shugaban kasar Grace Mugabe daga jam'iyyar baki daya. Yeukai Simbanegavi, ita ce shugaba kungiyar matasan jam'iyyar ta Zanu PF ta ce "Muna son a kori Grace Mugabe matar shugaban kasa daga jam'iyar kwata-kwata, kana shi Shugaba Mugabe ya sauka daga mukaminsa na shugaban jam'iyya da na kasa baki daya, ya je ya huta da kuma yi jinyar tsufansa"

Ita ma kungiyar tsaffin sojoji a Zimbabuwe ta gargadi Shugaba Mugabe da ya sauka daga mulki ba tare da bata lokaci ba, ko kuma sojoji su gama da shi tun a ranar Lahadi, ma'ana su saukeshi da karfin hatsi ko na bindiga. 

A ranar Lahadi ne aka tsara Shugaba Mugabe zai sake ganawa da shugabannin sojojin kasar da ke tsare da shi a gidansa a kokarin da ake na ganin ya sauka daga mulki ta hanyar laluma.