1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyu na ikirarin nasara a Senegal

Abdoulaye Mamane Amadou
August 2, 2022

Ana ci gaba da samun ra'ayoyin da ke cin karo da juna game da ikirarin lashe zaben 'yan majalisun dokokin kasar Senegal a tsakanin 'yan adawa da bangaren masu mulki.

https://p.dw.com/p/4Ez0y
Parlamentswahlen im Senegal
Hoto: Leo Correa/AP/dpa

Kawancen jam'iyyun da ke mulkin Senegal ta bakin Aminata Touré kakakin Shugaba Macky Sall, ta bayyana kawancen a matsayin wanda ya samu nasarar kujeru mafi rinjaye a zaben 'yan majalisa inda ya lashe yankuna 30 daga cikin 46.

Sai dai bangare kawancen "Yewwi Wallu" na jam'iyyun adawa sun yi fatali da haka, tare da bayyanawa manema labarai samun gagrumin rinjaye a zaben, da ke zaman zakaran gwajin dafi ga babban zaben shugaban kasa da ake shirin gudanarwa a shekarar 2024 da kek tafe.

Kawancen adawar dai ya kuma yi hannunka mai sanda game da duk wani yunkuri na murda sakamakon zaben don cin moraiyar bangaren jam'iyyun da ke mulki, yana cewa duk abinda zai biyo baya shugaba Macky Sall da 'yan koransa su kuka da kansu.