Majalisar dokokin Isra'ila ta amince da wanzuwar gwamantin haɗin kan ƙasa
May 9, 2012'Yan majalisar ta Isra'ila 71 ne dai su ka amince da wannan ƙawance tsakanin jam'iyyun biyu yayin da 23 su ka kaɗa ƙuri'ar rashin amincewa da shirin.
Sakamakon wannan matsaya da jam'iyyu biyun su ka cimma dai, yanzu haka Mr Netanyahu zai jagoranci 'yan majalisu 94, abin da ƙasar ta Bani Yahudu ba ta gani ba tun kusan shekaru 30 ɗin da su ka gaba.
Yanzu haka dai Shaul Mofaz zai yi aiki a matsayin mataimakin priyiministan ƙasar kuma ɗaya daga cikin jerin minitocin Isra'ila duk da dai ba a bayyana ma'aikatar da zai jagoranta ba.
Kafin 'yan majalisar su amince da wannan shirin da sai da aka tafka muhawara mai zafin gaske a zauren majalisar inda 'yan majalisar su ka yi ta yi wa Shaul Mofaz chari dangane da sauya ra'ayin da ya yi na shiga gwamnatin gamin gambiza bayan kuwa a baya ya bayyana cewar Benjamin Netanyahu maƙaryaci ne kuma ba zai taɓa yadda ya yi aiki da shi ba.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Umaru Aliyu