Ambaliya ta kashe mutane a Jamus
July 15, 2021Talla
Rahotanni sun tabbatar da samun tsaikon ababen hawa a wasu yankunan kasar sakamakon ruwan saman, matakin da ya shafi wasu harkokin yau da kullum, wasu da dama sun yi asara mai yawa.
Hukumomi sun ce akwai karin wasu gidaje 25 da ke fuskantar barazanar ruftawa a gundumar Schuld bei Adenau, an tura jami'an agaji domin zama cikin shirin ko ta kwana yayin da aka fara kwashe wasu jama'a a yankuna mafi hatsari.