Jamus da Faransa sun gargadi Ukrain kan siyasar kasar
February 23, 2016Talla
Ministocin sun yi wannan tsokacin ne a yayin da suke wata ziyara a kasar a inda suka jaddada zage dantse ga hukumomin kasar domin kawo karshen yakin 'yan awaren da ke a gabashin kasar.
Dukkanin ministocin harkokin kasashen biyu dai, sun kuma bukaci mahukuntan kasar fara aiwatar da wasu sabbin manufofin sauye-sauye da suka hada da tsari na dokokin zabe da yancin na musamman ga yankuna gami da yaki da cin hanci da rashawa.
Ziyarar ministocin ta zone kwana daya tak bayan da wasu mutane masu tarin yawa sun gudanar da wata zanga-zanga a birnin Kiev domin yin kiran murabus ga makaraban gwamnati tare da kiran gudanar da sabbin zabubbuka.