1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Dole a bai wa Falasdinu 'yanci

March 27, 2018

Gwamnatin Jamus ta sake jaddada matsayinta kan batun samar da kasashe biyu masu cikakken 'yanci, a matsayin abu mafi a'ala ga dorewar zaman lafiya a rikicin Isra'ila da Falasdinawa.

https://p.dw.com/p/2v2hb
Westjordanland Heiko Maas trifft Mahmoud Abbas
Hoto: picture-alliance/dpa7Zumapress

Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya sake jaddada matsayin Jamus kan samar kasashe biyu masu cikakken 'yanci, a matsayin abu mafi a'ala ga dorewar zaman lafiya a rikicin Isra'ila da Falasdinawa. Mr. Maas ya fadi hakan ne a jiya Litinin a wata ganawar da ya yi da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas da kuma ministan harkokin wajen Falasdinu a Ramallah.

Ministan na Jamus ya bukaci gwamnatin Falasdinun ta yi la'akain sanya Amirka a tattaunawar zaman lafiya da za a yi, saboda wuyar cimma nasara, muddin aka ware Amirkar. Amma fa shugaban Falasdinawan Mahmoud Abbas, ya yi watsi da shiga tasakanin Amirkar, musamman ta la'akari da ayyana birnin Kudus da shugaba Donald Trump ya yi cikin watan Disamabar bara, a matsayin fadar gwamnatin Isra'ila.

Su dai Falasdinawan na cewa ne gabashin birnin na Kudus shi ne zai kasance fadar gwamnatin da suke da'awar kafawa, koda yake shugaban na Falasdinawa ya yaba muhimmancin kasancewar Jamus da kungiyar EU a shirin samar da zaman lafiya tsakaninsu da Isra'ila.