1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Kashe-kashe na karuwa a Darfur

Abdullahi Tanko Bala MAB
April 29, 2022

Arangama kan ruwa da wurin kiwo a lardin Darfur na Sudan da bukatar 'yan Habasha na son zama sojan hayar Rasha saboda matsin tattalin arziki a kasarsu na daga cikin baututuwa da suka dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/4AdNq
Sudan - Unruhe
Kashe-kashe ya yawaita a yankin Darfur na kasar Sudan sakamakon rikicin kabilanciHoto: Rasd Sudan Network/AA/picture alliance

Za mu fara da jaridar Der Tagesspiegel wadda ta rubuta sharhinta a kan kashe-kashe da suka dawo a lardin Darfur na kasar Sudan. Jaridar ta fara da yin matashiya cewa a baya, batun satar dabbobi shi yake haifar da takaddama a lardin wanda kan kai ga zubar da jini da hasarar rayuka. Manoma 'yan kabilar Massalit sun zargi Larabawa makiyaya da korar musu dabbobi, su kuma suka kashe makiyaya biyu wajen daukar fansa. Wannan ya haifar da gagarumin tashin hankali inda a makon da ya gabata makiyayan suka kai hari a kauyen Massalit don daukar fansa. Rikicin ya yadu nan da nan wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 168 wasu fiye da 100 kuma suka samu raunuka.

Jaridar ta ce abin jiya ya dawo a Darfur. 

Rikicin yankin Darfur da aka kwantar da shi bayan kawar da gwamnatin Al Bashir ya sake dawowa. Lamarin da ya faru a baya bayan nan na kama da rikicin da ya auku a 2003 lokacin da yakin basasa ya barke a Darfur tsakanin Larabawa da al'ummar yankin na Darfur, kuma har yanzu tushen rikicin na zama kan albarkatu a yankin na Sahel da ke fama da kanfar ruwa da abincin dabbobi wato ciyawa.

Äthiopien Addis Abeba | Schlange vor der Russischen Botschaft
Matasan Habasha na dandazo a kofar ofishin jakadancin Rasha a birnin Addis Ababa,Hoto: Seyoum Getu/DW

'Yan Habasha na son zama sojan hayar Rasha.

'Yan Habasha na son zama sojan hayar Rasha saboda matsin tattalin arziki a kasarsu. Wannan shi ne taken sharhin jaridar die Tageszeitung. Jaridar ta ce maza 'yan Habasha na neman aiki mai gwabi na yakin da Rasha ke yi da Ukraine saboda sun saba da makaman Rasha. Akwai daruruwan matasa wadanda a kullum suke yin dandazo a kofar ofishin jakadancin Rasha a birnin Addis Ababa, yawancinsu dauke da takardunsu na neman aiki da kuma shaidar kammala makaranta da na horon da suka samu na aikin soji.

Kasar Habasha dai na da alaka da Rasha tun zamanin tarayyar Soviet a shekarun 1980. Yawancin sojojin kasar sun samu horo ne a Rasha kuma har kawo yau galibin makamansu kirar Rasha ne. Ofishin jakadancin Rasha a Addis Ababa ya fidda sanarwa a ranar 19 ga wannan watan na Afrilu inda ya yaba da goyon bayan matasan na Habasha, yana mai cewa wannan ya nuna dangantaka mai karfi da aminci da kuma abokantaka da alakar taimakon juna a tsakanin al'umomin kasashen biyu.

A bangarenta gwamnatin Habasha ta yi maraba da sanarwar. Sai dai ta ce daukar 'yan kasarta aikin sojan haya ya saba wa ka'idar aikin ofishin jakadanci. Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta kara da cewa daukar 'yan kasar Habasha su yi yaki a wata kasa ta waje haramun ne.

BG I Fotoausstellung „40 Jahre laif – 40 Positionen dokumentarischer Fotografie“ I Köln
A tashar jirgin ruwa na Accra, ana sauke tsoffin kayayyaki da suka hada da kayan latroni Hoto: Kai Loeffelbein/laif

Afrika na gadon sharar Turai

Ita kuwa Jaridar Die Welt tsokaci ta yi da cewa Afirka na gadar shararmu ma'ana shara daga tarayyar Turai, Jaridar ta ce muna samar da tarin tsoffin kwamfutar laptop da firinji da tsoffin talabijin wadanda ke karewa a can tare da yin illa ga mutane da kuma muhallin yankin. Jaridar ta yi tambayar cewa ta ya ya za a magance wannan?

Kamar sauran kasashe masu tasowa na Afirka, kasar Ghana ba ta da cikakken tsarin sarrafa shara. Bugu da kari a tashar jirgin ruwa na Accra, ana sauke tsoffin kayayyaki da suka hada da kayan latroni da tsoffin motoci da firinji da sauran na'urori. Dokokin kungiyar Tarayyar Turai dai sun hana zubar da irin wadannan kayayyaki barkatai, amma a tashar Agbobloshie da ke Ghana babu ingantaccen tsarin sa ido.

Mutane kimanin 4000 nesuke aiki a bolar tattara sharar, yawancinsu cikin hadarin shakar sinadarai masu guba da ke fitowa daga na'urorin. A shekarar 2016 gwamnatin Jamus ta hannun hukumar raya kasashe BMZ da hukumar kawancen bada taimako ta kasa da kasa ta Jamus GIZ sun taimaka wajen bada tallafi ga kasar Ghana da kuma horo kan alkinta sharar da sarrfata.