Majalisar Jamus ta yi tir da kyamar Yahudawa
May 19, 2021Talla
A yayin zanga zangar adawa a fadin kasar a game da abin da ke faruwa tsakanin Israila da Falasdinawa 'yan sanda sun tarwatsa gangamin nuna kyama ga Yahudawa da kuma tsaurara mnatakan tsaro a wuraren ibadar Yahudawa.
Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya bukaci daukar tsauraran matakai akan masu akidar nuna kyamar Yahudawa da kalaman kiyayya da kuma masu haddasa tarzoma.
Ya kuma yi kiran kawo karshen hare hare akan Israila tare da bukatar tsagaita wuta da kuma yin tattauna kai tsaye tsakanin Israila da Falasdinawa don samun masalaha